MINBARIN MUJI MU KARU

NA SADAUKAR DA SHAFIN NAN GA KAKANA LIMAMIN DAURA USMAN (1899)

KUNDI TARIHI

view:  full / summary

KO MENENE SILA? By ibraheem self seeker islam

Posted by IBRAHEEM UTHMAN YOUSUF on July 27, 2012 at 10:40 PM Comments comments (0)
Kullum zuciyata cike take da abin mamaki dan gane da rayuwar malam bahaushe a yanzu. Yanda malam bahaushe yayar da al'adunsa yake kokarin kama al'adun turawan yamma, duk da yake wannan alama ce ta karshen duniya amma ko kadan malam bahaushe yaki ya fiskanto meke masa zafi arayuwarsa. A koda yaushe komai kara raguwa yake a al'adun malam bahaushe. Ada yanda akasan duk wani bahaushe yana da abubuwa kamar haka:- 1- Mai jajircewa ne akan addininsa na musulunci. 2-kamili ne mai kare mutunci ta bangare da dama. 3-Mai kokarin ganin ya kyautatawa dan uwansane. 4-Mai matukar tausayine ga yan uwansa hausawa kai harma da wadanda ba hausawanba. 5-Mai son ganin cigaban kabilarsane ako wane yanayi ya tsinci kansa na mulki. 6-Mai tarbiyane irin ta addinin musulunci. 7-Mai kokari matuka ta bangare kasuwanci da sana'o'i. 8-Malam bahaushe yana girmama iyayensa matukar girmamawa tare da abokan iyaye da makotansa. 9-Mai matukar girmama shugabanine muddin shugaba bai taka Addinin da Al'adar sa ba, amma ta musulunci. 10-Mai watsine da al'adun maguzanci da ya riska a da kafin zuwan musulunci. Dadai sauransu da dama wanda idan zan lissafosu sai dai in wallafa littafi babban gaske. Amma kash yanzu malam bahaushe ya watsi da wadannan ababen dana lissafo dama wadanda ban fadosu ba, abin tambaya anan shine ko KO MENENE SILA? Nidai a harshashen na yaro matashin da bai wuce shekaru 22 ba, wanda shima ya tsinci kansa wajen bada goyon baya n watsar da al'adun bahaushe ta sigogi daban daban, wanda karshe abin yai min ciwon gaske harma na fuskanto kura kuraina, harma nake ko karin na gyarasu. Ina ganin cewa Zuwan Ilimin boko ne ya tabarbarar mana da da Al'adunmu, domin mun amshi ilimin a maguzance yanda yazo mana daga yammaci duniyar batare da mun musuluntar dashiba. Aganina wannan ba karamar asarace muka tafka ba, domin yanzu haka dawo da mutuncinmu irin na addini musulunci yana da matukar wuya sai dai kawai mu tsunduma INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN Domin tarbiyar malam bahaushe ta watse koyarwar da malam bahaushe ya koya tunda iyaye da kakanni ta watse, a yau ne wai a kano ne zaka samu yara matasa irin mu, sun dauki al'adun maguzawan yamma sun cusa kansu a ciki wai su hakan da suke ganin sun sa kansu a ciki wai waye wace. Haba hausawa kuna gani yayayenku maza da matansu sun goge sun zama tamkar yahudawa, a yaune a wannan zamaninne ake samun yaduwar fasikanci da yawaitar zina da wulakantar da darajar yaya mata ta hanyoyi daban daban. Wai ayaune ya mace take ganin tafi iyayenta sanin duniyarnan, sukuma iyayen suna kallonsu tamkar ba iyayensuba. Ya yan uwana musulmai kudu ba kuga yanda yan uwa musulmai matasa suke mazan su da matan su, suka tsinci kansu a cikin watsi da koyarwar Allah da manzonsa. Gabaki daya mutanen mu yanzu gani suke inbakai shigarsu oo ba bakawaye ba, haka ma yanzu ganin suke idan bakya zina ko luwadi ko madigo ga baki daya baki wayeba, yin hakan zai nuna musu bakije makarantar boko ba. Kai wannan rayuwa tana cike da abubuwa maras kyau da gurbatar tarbiya. Allahu akbar, dukkan abubuwan da suke faruwa ayanzu a fadin nahiyar arewan hausawan najeriya, musulunci yazo dasu kuma yazo da warakar su to babban abin duba shine mai zai hana masu mulki da malaman addini damasu fada aji suyi kokarin kawo gyara? Kash! Saidai sukansu masu mulkin da masu fada ajin da wasu malaman ba abinda ya shafesubane, sudai burinsu kawai kullum shine yaki haram yaki halak. Hatta wasu malaman jahilci yai musu yawa ko kuma sun sani suke take sanin dandai su gina rayuwarsu ta duniya a maimakon ta lahira, wai a arewa ne garin musulunci zakaji dan siyasa ya fito agidajen yada labarai yana cewa wai "idan ba a yi dimokaradiyaba wallahi baza asamu zaman lafiya ba" wannan wane sakarci ne da jahilci da rashin sanin me addini yakoyar mai magabata na kwarai suka gabatar . Wannan yanuna sukansu wakilan namu na gwamnati a kwai karanci ilimin addini akansu. Akan haka nake kira ga malam bahaushe ya tashi ya zage damtse ya nemi ilimin addini dana zamani domin kawo gyara a bangaren da yake ganin akwai maguzanci turawan yamma ta cin fuskar koyarwar Allah(SWT) da manzonsa annabi Muhammad(SAW). Nine dan uwanku IBRAHEEM SELF SEEKER ISLAM.

LALLAI NAYI WAUTA AKAN SOYAYYAR 2GO DANAI DA KHALEESAT ASHE NA MIJINE KUMA ABOKIN SHAWARATA. By ibraheem self seeker islam

Posted by IBRAHEEM UTHMAN YOUSUF on July 27, 2012 at 12:20 PM Comments comments (1)
Ranar lahadi karshen watan mayun shekarar nan ne ta 2010, na tsinci kaina a shafin hirar nan wanda yai kaurin suna a Nijeria wata '2GO', hakan ya farune don kawai kuri danayi na cewar BA YANDA ZA'AI NAI HIRA DA MUTUM HAR TA TSAWON MINTI 30 BATARE DA NA BANBANCE JINSINSABA KO DA KUWA YA KARYAR SA JINSINSA. Domin ni aganina nagama sanin dukkan wani salo da taku na ya mace da kuma halin da na miji. Aiko dai na tsinci kaina a cikin kuri da dagawa akan hakan har abokaina suke cemin wallahi ban isa ba. Domin akwai mazan da suka kware a wajen hira irin ta yaya mata. Na allanfur cewa wallahi ba da namiji daya isa ya yaudareni a 2go a matsayinsa na da namiji akai musu sosai akan hakan fiye da kwanaki shida ana ta taburza akan hakan, ina cewa karyane. Kwatsam, safiyar Lahadi farkon watan April, na dauko wayata na bude shafin hirata na 2go, sainaga an aiko min da request din cewa anasona da abokantaka, na duba mai request din naga sunan mai requesting din khaleesat__ nai farin cikin ganin mace ce take son zama abokiyata. Cikin sauri nai accepted dinta amma kash! Alokacin bata kai ma'ana offline. Ban damuba domin nasan duk yanda akai jiya ne aka turo min da wannan sakon. Yammaci ranar lahadin ina zaune tare da abokaina muna chamber sai na dauko dauko wayata kai tsaye na nufin shafin hirata na 2go, shi gata ke da wuya sai na tarar da ita bata kai, nai bakin ciki matuka amma sam abokaina basusan me ke faruwa ba, can sai naji karar anyi joinin ma'ana abokina wani yahau nai saurin fitowa daga hausa rum aiko sai na sa'ar gani khaleesat akai na tura mata da welcome ta basar kamar mace mai jan aji, sai ta amsa min, muka tsunduma da hira, har mukai matukar nisa a hira, take nuna min cewa ita bakuwa ce a shafin hirar 2go din, muna ta faman hira kwatsam sai ta fara kirana da yaya islam, abin ya dauremin kai matuka, muka ci gaba da hirar kusan kimanin awarmu biyu muna hira. Saitace min zata sauka, nace mata to mukai sallama, ta sauka. Ni kadai sai akaga ina ta dariya, sai abokaina suke tambayata, menene? Nace wallahi wata baiwar Allah na samu mai suna khaleesat kuma mutuniyar bichi local govt. Ce dake nan jihar kano. Sukaimin farin ciki, suka nuna min sam basuda masaniya akanta. Sai daya daga cikinsu yace min na basu username dinta sunason abokantaka da ita, nan naki yarda na basu, kuma na shiga taka tsam tsam da wayata gudun karsu daukar min username dinta. Acikin kwanaki biyar muka yi shakuwar da ta kusa tasani cikin halin tagayyara a rayuwa kullum cikim soyayya mai matukar ban mamaki, sai take tambayata hotona nace to amma sai ta fara turo min nata amma tace min wai dole saita fara ganin nawa nace wannan mai saukine na tura mata, hoto daya daga cikin hotunana, na tambayeta tagani ta cemin eh! Sannan tace min gana ta nan zuwa. Kawai sai ga sako. Na duba kawai sai naji wani irin dadi a zuciyata domin ganin danai kyakykyawa ce ta musamman ba irin sauran mata ba. KASH! Mai karatu muhadu a blog nagaba Daga ibraheem self seeker islam

Rss_feed